Barcelona za ta yi nazari kan kara wa Messi albashi

Babban jami'in Barcelona, Oscar Grau, ya ce kara wa Lionel Messi kudin sabuwar yarjejeniya zai danganta ne da karin kudin shiga daga masu daukar nauyin kungiyar.
A shekarar 2018 yarjejeniyar Messi za ta kare, ana kuma ake jin zai bukaci a kara masa kudi a sabon kwantiragin ta yadda zai yi daidai da wanda aka bai wa Luis Suarez da Neymar na fam miliyan 21 a shekara.
Sai dai, a cewar Grau matakin La Liga na kayyade albashi na nufin sai Barcelona ta yi dogon tunani.
La Liga kan cimma yarjejeniyar iyakance albashi da ko wacce kungiya a farkon kakar wasanni, lamarin da ke hana hukumomin kungiyoyin kashe kashe fiye da kaso 70 cikin 100 na kasafin kudinsu a kan biyan albashi.
Messi mai shekara 29, yana karbar fam miliyan 19, kuma Grau ya ce idan har za a karawa Messi albashi suna bukatar yin nazari mai zurfi.