FA ta kara wa Man City lokacin amsa tuhuma

Gasar Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bai wa City zuwa ranar 27 ga watan Janairu domin ta kare kanta

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kara wa Manchester City lokaci domin ta amsa tuhumar da ta yi mata kan gaza samar da bayanai kan gwajin shan abubuwa masu kara kuzarin 'yan wasanta.

Hukumar ta tuhumi Manchester City da kasa tabbatar wa wakilan da ke gwada 'yan kwallo kan shan abubuwa masu kara kuzari da bayanan inda 'yan wasanta suke zuwa.

A dokance an umarci kungiyoyi su bayar da bayanan yadda take yin atisaye da kuma wuraren da 'yan kwallo ke zuwa, domin a gwada su idan an bukaci hakan.

Manchester City ta kasa bayar da cikakkun bayanai kan yadda 'yan kwallonta ke yawace-yawacensu.

A can baya hukumar ta bai wa kungiyar zuwa 19 ga watan Janairu domin ta kare kanta, yanzu ta maida shi zuwa ranar 27 ga watan Janairun.

Manchester City tana mataki na biyar a kan teburin Premier da maki 42 bayan da ta yi wasanni 21 a gasar.