An ladabtar da sojojin da suka ci zalin gurgu a Najeriya

Nigeria army Hakkin mallakar hoto @HQNigerianArmy
Image caption Gurgun da sojojin suka ci zarafinsa, Chijoke Uraku

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ragewa wasu jami'anta biyu girma wadanda a ka gansu a wani bidiyo suna cin zalin wani nakasasshe a jihar Anambra dake kudu maso gabashin kasar.

Sojojin da aka rage wa matsayin su ne Kofur Bature Samuel da Kofur Abdulazeez Usman.

Bayan an kama sojojin biyu, an musu shari'a cikin gaggawa inda aka same su da aikata laifuka biyu.

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya ce an ragewa sojojin girma zuwa kurata, sannan za su yi zaman gidan kaso na kwanaki ashirin da daya da aikin karfi.

Kazalika Kukasheka ya ce sojojin ba za su samu albashinsu ba na kwanaki ashirin da daya ba.

Ya ce rundunar sojin ta kuma gana da nakasasshen da aka ci zalun na shi, Chijoke Uraku.

Rundunar sojin Najeriyar ta jaddada kudurinta na tabbatar da dakarunta suna aiki da doka da oda a kowanne lokaci.

Dama dai, kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sha zargin sojojin Najeriya da take hakkin mutane, zargin da rundunar sojin kuma ke yawan musanta wa.