Zanga-zangar kyamar Trump a Mexico

An gudanar da zanga-zanga kan manufofin Trump a Mexico
Image caption Shugaban Amurika Donald Trump

A cikin titnunan manyan buranan kasar ta Mexico sama da guda 10,duban 'yan kasar sun gudanar da zanga-zanga.

Masu zanga-zangar na nuna adawar su game da manufofin Shugaba Trump na Amurka kan bakin haure da kuma manufarshi ta sanya kasar biyan kudin gina katanga kan iyaka tsakanin Amurika da Mexico .

Da dama daga cikin masu zanga-zangar su na sanye da fararan tufafi, tare da nuna tutocin kasar ta Mexico , wasu na dauke da alluna da aka rubuta kalmomin na nuna kyama ga shugaba Trump cikin yaran Spaniyanci da kuma Inglishi.

Zanga-zangar dai ta kasance kamar askin wanzaman dare, wanda bai bar kowa ba.

Wato kuma, masu zanga zangar sun yi ta kalamai marasa dadi zuwa ga shugaban kasar ta Mexico, Enrique Pena Nieto,wanda su ke zargi da kasancewa Musar Lami, ba shi da wani kuzari da ya ke nunawa , abun da ya sa bai yi wanni katabure ba , wajen kawo karshen cin hanci da rashawa da suka zaman ruwan dare a cikin kasar.

Haka ma, ya kasa kawo karshen tashe -tashen hankulla da suka adabi jama'a.

Masu zanga-zangar dai sun ce ,wannan sako ne su ke aikawa ga shugaba Trump.Kuma ya sani 'yan kasar Mexico, sun hada kansu su yaki manufofinshi, tare da goyon bayan 'yan Mexicon da ya ke son ya tiso keyarsu daga Amurika ba tare son su ba.