Ozil ba shi da karfin hali — Wenger

Arsenal Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan Arsenal na tsakiya Mesut Ozil

Arsene Wenger ya ce dan wasan Arsenal na tsakiya Mesut Ozil na fama da matsalar rashin kwarin guiwa da karfin hali bayan da ya yi wasa takwas bai ci kwllo ba.

Wenger, wanda kungiyarsa za ta ziyarci Bayern Munich ranar Laraba, domin wasan cin kofin Zakarun Turai, zagayen kungiyoyi 16, ya ce, bai san dalilin da ya sa dan wasan ba ya kokari ba yanzu.

Kocin ya ce, kila zai dawo kan ganiyarsa, saboda akwai hare-hare da dama da yake kaiwa, ba ya sa'ar cin kwallon.

Ozil bai ci kwallo ba a manyan wasannin Arsenal takwas da ta yi, tun lokacin da a gida ta doke Stoke 3-1 a watan Disamba, nasarar da ta sa kungiyar ta hau kan teburin Premier a lokacin.

A kwanan nan Ozil wanda Arsenal ta kashe fan miliyan 42 wajen siyo shi daga Real Madrid a shekarar 2013, ba ya taka wata rawar a-zo-a-gani a kungiyar.

A bana Ozil ya ci kwallo biyar ne a Premier, sabanin shida da ya ci a gasar a bara, kakar da ya fi kokari a kungiyar ta Arsenal.