Dole jami'anmu su daura dankwali a Iran - Sweden

sweden Hakkin mallakar hoto Irna
Image caption A makon jiya ne ministar kasuwanci Ann Linde ta jagoranci wata tawaga

Gwamnatin Sweden ta kare wani mataki da ta dauka na barin jami'anta su daura dankwali a lokacin da suka yi wata tafiya zuwa Iran.

Gwamnatin ta ce rashin yin hakan na nufin an karya doka.

A makon da ya gabata ne Anne Linde, Ministar kasuwancin Sweden din ta jagoranci wata tawagar 'yan kasuwa kuma ta sha suka saboda ta saka dankwali.

Sweden ta ce ita ce gwamnati ta farko a duniya mai fafutukar kare ra'ayin mata.

Wata 'yar siyasar Sweden kuma fitacciyar mai fafutukar kare hakkin mata ta soki wannan mataki.

"Shawarar za ta yi illa ga abin da ake kira manufar kasashen waje mai ra'ayin mata," a cewar Jan Bjorklund na jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi.

Ya kuma kara da cewa Iran tana danne hakkin mata ta hanyar dokoki.

Mista Jan ya ce kamata ya yi a ce gwamnatin Sweden ta bukaci cewa matan da ke cikin tawagarta ba za su saka dankwali ba.

Ya kara da cewa idan har kuma Iran din bata yarda da hakan ba, sai a saka hannu a yarjejeniyoyin kasuwancin a Sweden din ko kuma a wata kasar daban.

Amma Ms Linde ta shaidawa jaridar Aftonbladet cewa ba ta so ta karya dokar Iran.

Ta ce tun da zabin da suke da shi kawai, shi ne su tura tawagar maza, sai aka bukaci ta saka dankwali.

Stefan Lofven, firai ministan Sweden ya ce shi ma ya je Iran din kuma ya tattauna batun 'yancin dan adam da shugaban Iran din Hassan Rouhani.