Adama Barrow zai saɓi rantsuwar kama aiki karo na biyu

Adama Barrow Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sa ran dubban mutane ne za su halarci bikin rantsuwar karo na biyu

Sabon shugaban Gambia, Adama Barrow zai saɓa rantsuwar kama aiki a karo na biyu a ranar Asabar bayan Yahya Jammeh wanda ya mulki kasar sama da tsawon shekara 20, ya fice a cikin watan jiya.

Bikin rantsuwar ya zo daidai lokacin da Gambia ke cika shekara 52 da samun 'yancin kai.

Ana sa ran dubban mutane ciki har da shugabannin Afirka da dama za su halarci bikin rantsuwar a babban filin wasan ƙasar da ke Banjul.

An rantsar da shugaba Barrow a wani dan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka yi a cikin Senegal mai makwabtaka, kafin mutumin da ya kayar, Yahya Jammeh ya sauka daga mulki.

Sai da manyan ƙasashen Afirka ta yamma suka tura sojoji don tabbatar da ganin Jammeh ya bar mulki bayan tun da farko ya sauya magana a kan sakamakon zaben watan Disamba.

Tuni dai aka saki fursunonin siyasa da dama yayin da ƙasar ke shirin sake shiga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da kuma ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila.

Labarai masu alaka