NDLEA ta kama kwanso 73 na Cocaine

An kama mutumin da ya yi yunkurin fita da hodar ibilis din ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
Image caption An kama mutumin da ya yi yunkurin fita da hodar ibilis din ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama wani mutum da kwanso saba'in da uku na hodar ibilis ta Cocaine, yayin da yake yunkurin fita daga Nijeriya zuwa Dubai, dake Hadaddiyar Daular Larabawa.

An kama mutumin mai shekara 49 ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja babban birnin Nijeriya yayin binciken matafiya.

Wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar ta NDLEA, Ofoyeju Mitchell, ya raba wa manema labarai, ta ce mutumin ya yi kashin dauri 73 na hodar ta Cocaine ne yayin da ake bincikensa, kuma nauyinsu ya kai kilogaram 1.699.

Hukumar ta ce mutumin mai suna Nwafor Samson Tochukwu, dan asalin jihar Anambra ne, mazaunin Legas, ya kuma shaida mata cewa ya shiga harkar fataucin muggan kwayoyin ne saboda da matsin tattalin arziki.

Sanarwar NDLEA din ta kuma ce mutumin wanda ainihin sana'arsa ita ce sayar da kayayyakin aikin ofis, ya yi ikirarin cewa wasu ne suka ba shi naira miliyan daya da dubu dari biyar don ya yi masu fataucin kwayoyin zuwa Dubai, amma yanzu yana nadama bayan kama shi.

Hukumar ta NDLEA dai ta ce zata gurfanar da mutumin da ake zargi a gaban kotu nan ba da dadewa ba, inda zai fuskanci yiwuwar hukuncin daurin rai-da-rai kamar yadda dokokin Najeriya suka zayyana.

Labarai masu alaka