Venezuela ta kira shugaban Peru Kare kuma matsoraci

Shugaban kasar Peru Pedro Pablo Kuczynski
Image caption Shugaban kasar Peru Pedro Pablo Kuczynski

Gwamnatin Peru ta bukaci jakadanta da ke Venezuela da ya dawo gida bayan sabanin diplomasiyya da aka samu tsakanin kasashen biyu.

Mahukunta a kasar sun aike da wasika dauke da kalamai marassa dadi bayan da ministan harkokin wajen Venezuela ya kira shugaban kasar Peru din matsoraci kuma Kare wanda ke biyayya ga Amurka.

Peru ta ce ba zata lamunci wulakanci da cin zarafi ba.

A wata ziyara da ya kai kwanan nan Amurka, Shugaban kasar Peru,Pedro Pablo Kuczynski ya ce Venezuela babbar matsala ce a garesu da ma Amurkan baki daya.

Tuni dai shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya nemi afuwa a kan wadannan kalamai.

Labarai masu alaka