Takaddamar Kwastam da Majalisa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sabuwar dambarwa

A yayin da 'yan majalisar dattawan Najeriya ke takun-saka da shugaban hukumar Kwastam a kan harajin shigar da motoci kasar, alamu na nuna cewa wata sabuwa kuma na gab da kaurewa tsakaninsa da majalisar wakilai.

A wani zaman da suka yi, wasu 'yan majalisar na zargin hukumar da yin tafiyar-hawainiya wajen yin gwanjon kayan da jami'anta suka kama, wadanda suke jibge a tasoshin ruwa da wasu sassa.

Honorabil Garba Hammanjulde Garba-Chede, mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan ayyukan kwastam, ya yi wa Ibrahim Isa karin bayani.