Shin Buhari zai cire Ibrahim Magu?

Ibrahim Magu Hakkin mallakar hoto Efcc
Image caption Ibrahim Magu ya ce masu tsoron aikin da yake yi ne ke son a cire shi

Wa'adin da majalisar dattawan Najeriya ta bai wa shugaban kasar Muhammadu Buhari na mako biyu domin ya cire shugaban hukumar EFCC, mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, Ibrahim Magu, wata babbar alama ce da ke nuna cewa an ja layi tsakanin fadar shugaban kasar da kuma masu yi wa kasar dokoki.

'Yan majalisar dai sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda Shugaba Buhari ba ya mutunta kudurce-kudurcen da suka zartar.

Sun bayar da misalin cewa duk da yake sun dade da zartar da hukuncin kin tabbatar da shugaban na EFCC kan mukaminsa bisa yin la'akari da rahoton da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta fitar inda ta zarge shi da aikata wasu laifuka, amma shugaban ya yi burus da bukatar sauke Mr Magu.

Koda yake yanzu ministan watsa labarai ya ce an kafa kwamitin da zai yi sulhu tsakanin bangaren zartarwa da na masu yin dokoki.

Ita dai DSS ta ce an kama shugaban riko na EFCC ne da laifukan da suka hada da tafiya da fayil-fayil na hukumar gidansa tun lokacin shugabancin Madam Farida Waziri, tsohuwar shugabar hukumar -- laifin da, a cewar hukumar da ke sa ido kan ayyukan 'yan sanda, yake na biyu mafi girma idan ban da kora daga aiki.

Haka kuma an zargi Mr Magu da bai wa wani amininsa, wanda DSS ke zargi da almundahana Air Commado Mohammed Umar wasu takardun sirri na EFCC baya ga hada baki da shi wurin karbar gidan da hukumar babban birnin tarayya ta kamawa Mr Magu domin ya zauna lokacin da aka nada shi kan mukaminsa.

An wanke shi

Sai dai masu sharhi da dama da kuma ma 'yan kasar na mamakin yadda DSS da 'yan majalisar dattawan suka nace kan sai an cire Ibrahim Magu daga kan mukaminsa duk da yake tuni ministan shari'a Abubakar Malami ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen da aka yi masa.

Ministan ya yi bincike kan wadannan zarge-zarge ne bayan shugaban kasa ya ba shi umarnin yin hakan a watannin da suka gabata.

Shi kan sa shugaban na EFCC ya sha musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa mutanen da ke da kashi a gindi ne ke son shafa masa kashin shanu.

A wata hira da ya yi da BBC, Ibrahim Magu ya ce: "Akasarin mutanen da ke wadannan zarge-zarge suna yin haka ne saboda su hana mu yakin da muke yi da cin hanci da rashawa".

A cewarsa, mutanen, wadanda akasarinsu na da korafe-korafe a kansu game da cin hanci da rashawa, sun jajirce domin ganin bai kai labari ba.

Akwai ƙanshin gaskiya

Masu sharhi a kan harkokin siyasa sun ce dirar-mikiyar da 'yan majalisar dattawan da kuma hukumar DSS suka yi wa Mr Magu ta nuna cewa akwai jan aiki a yunkurin da shugaban kasar ke yi na kakkabe cin hanci da rashawa daga Najeriya.

Dr Abubakar Kari, Malami a Sashen nazarin kimiyar siyasa da ke Jami'ar Abuja, ya shaida min cewa: "Akwai matukar daure kai dangane da yunkurin da ake yi na cire Ibrahim Magu. Kar ka manta, an wanke shi daga dukkan zargin da ake yi masa. Don haka a ganina wadanda ke son cire shi ba su da akida irinta shugaban kasa ta yaki da cin hanci."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu na ganin shugaban DSS Lawal Daura ba ya ga-maciji da Mr Magu

Dr Kari ya ce bai yi mamaki kan nacewar da DSS da 'yan majalisar dattawa ke yi don ganin an kawar da shugaban riko na EFCC ba, yana mai cewa "kar ka manta cewa yawancin 'yan majalisar nan tsofaffin gwamnoni ne wadanda ake zargi da sace kudin jihohinsu kuma da ma EFCC na bincikensu. Baya ga haka, shi kansa Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki Mutum ne da tun da aka soma wannan gwamnati yake dabaibaye da zarge-zargen cin hanci da almundahana. Kuma yanzu haka ana yi masa shari'a; don haka ba abin mamaki ba ne idan suka Ki amincewa da Magu".

Sai dai ya ce bai kamata shugaba Buhari ya yi gum da bakinsa kan wannan batu ba.

Ya ce: "Ni a ganina bai kamata shugaban kasa ya yi shiru ba; ya kamata ya sani cewa wasu na barazana da yakin da yake da cin hanci kuma idan har ya amince aka cire Ibrahim Magu, kasashen wake da ke yaba masa kan wannan yaki da ma 'yan kasar za su ga cewa lallai ba da gaske yake ba."

Labarai masu alaka