Makiyaya sun kona wani gidan gona a Kenya

Mukutan Hakkin mallakar hoto The Star Kenya
Image caption Gidan gona na Mukutan shi na an lalata wani bangare na shi

Makiyaya da ke ci gaba da shiga gonakin mutane a tsakiyar Kenya sun banka wa wani babban gidan gona wuta, a yunkurin ganin sun kauce wa kamen 'yan sanda.

Rahotanni sun ce makiyayan sun banka wa gidan gonar wuta ne a matsayin ramuko ga zargin kashe musu dabbobi da 'yan sanda suka yi.

Makiyayan sun kona gidajen kwanan baki biyu a gidan gonar Laikipia Nature Conservancy.

Baya ga zargin kashe musu dabbobi, makiyayan suna kuma zargin 'yan sanda da tilasta musu ficewa daga gandun daji da suke kiwon dabbobinsu.

Sai dai 'yan sanda sun ce dabbobin makiyayan sun mutu ne sakamakon musayar wuta da makiyayan, wadanda suke amfani da dabbobin a matsayin garkuwa.

Makiyayan dai sun rika shiga gidajen gona da gandun daji da aka kebe ne domin kiwon dabbobinsu saboda matsanancin fari da ake fama da shi a sassan kasar.

A watan jiya ne 'yan sanda suka kaddamar da fafutukar korar makiyayan daga gonakin, lokacin da wasu daga cikin makiyayan suka harbe wani mai gidan gona dan kasar Burtaniya.