'Ina zargin da aka yi wa Abba Kyari ya kwana?'

Abba Kyari da tare da tsohon jakadan Amurka a Nijeriya Entwistle Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abba Kyari na da ƙarfin faɗa-a-ji a fadar gwamnatin Nijeriya

Wasu 'yan Nijeriya na ci gaba da tambayar ko me ya sa ba a haɗa da wasu jami'ai kamar Malam Abba Kyari a dakatarwar da shugaban ƙasar ya yi wa wasu manyan jami'ansa biyu ba?

Matakin dai ya biyo bayan umarnin da shugaba Muhamadu Buhari ya bayar na dakatar da sakataren gwamnatinsa da babban jami'in hukumar leƙen asirin ƙasar ta NIA don a binciki zargin da ake yi musu,

Shi dai, shugaban ma'aikatan na fadar shugaban ƙasa, kurarsa ta yi kuka ne, lokacin da wasu kafofin yada labarai suka zarge shi da karɓar toshiyar bakin Naira miliyan 500 daga kamfanin sadarwa na MTN don a sassauta tarar da gwamnati ta yi masa.

Abba Kyari dai bai fito fili ya musanta zargin ba a lokacin, sai dai Shugaba Buhari ya gargaɗi masu zarge-zargen su daina, matuƙar ba su da shaidar da za ta tabbatar da haka.

Mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Malam Garba Shehu ya ce a iya saninsu hukumomi sun yi bincike kuma an wanke Abba Kyari.

'Reshe zai juye da mujiya'

A cewarsa shi kansa kamfanin MTN ya fito da sanarwa da ke musanta zargin da ake yi masa na bayar da toshiyar baki. "Saboda haka, an wanke shi," in ji Garba Shehu.

Ya ce ƙarshenta dai reshe zai juye da mujiya, don kuwa shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Nijeriyar ya rubuta takarda zuwa ga hukumomin tsaro inda ya buƙaci su bi masa kadi.

Mai yiwuwa ne sai maganar ta dangana da zuwa kotu, in ji mai magana da yawun fadar shugaban Nijeriya.

Da aka tambaye shi, ko akwai ƙarin wasu manyan jami'an gwamnati da za a sake bincika kan zargin almundahana? Garba Shehu ya ce ai kowa ma a yanzu an sa ido a kansa.

Ya ce a yanzu haka ofishin mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro ya ƙara sanya idanu a filayen jirgin sama na ƙasar don kama kuɗaɗen da ake sulalewa da su.

Labarai masu alaka