Kofin FA: Arsenal ta yi waje da Man City

Alexis Sanchez lokacin da ya ci kwallon Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sanchez wanda ya ci wa Arsenal ta biyu, ya kuma ci mata a wasan dab da na kusa da karshe da Lincoln

Arsenal ta yi waje da Manchester City da ci 2-1 a wasan kusa da karshe na Kofin FA, a Wembley, inda ta kai wasan karshe a karo na uku cikin shekara hudu.

City, wadda dan wasanta David Silva ya ji rauni tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, ita ta fara zura kwallo a raga ta hannun Sergio Aguero a minti na 62.

Sai kuma Nacho Monreal ya rama wa Arsenal a minti na 71, duk da harin da Yaya Toure ya kai da kwallon ta daki sandar raga, da kuma wanda Ferrnandinho ya buga ta daki saman sandar raga, haka aka juya zuwa lokacin fitar da gwani 1-1.

A kashin farko na lokacin raba-gardamar ne Alexis Sanchez a minti na 101 ya jefa kwallo ta biyu ragar 'yan City bayan da suka kasa kawar da kwallon da Mesut Ozil ya shirgo a bugun tazara.

Yanzu Arsenal za ta kara da Chelsea a wasan karshe a filin wasan na Wembley ranar Asabar, 27 ga watan Mayu May.

A ranar Asabar ne Chelsea ta doke Tottenham 4-2 a daya wasan na kusa da karshe, wanda hakan ya sa ta samu wannan dama ta daukar kofuna biyu na FA da kuma na Premier a bana.