'Fari da yunwa ne ke janyo fashin jirgi a Somalia'

A 'yan kwanakin nan fashin teku na karuwa a gabar tekun Somalia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 'yan kwanakin nan fashin teku na karuwa a gabar tekun Somalia

Wani babban jami'i a rundunar sojin Amurka ya ce karuwar fashin jirgin ruwan da ake samu a gabar tekun Somalia a 'yan kwanakin nan baya rasa nasaba da fari da kuma yunwar da ake fama da ita a kasar.

General Thomas Waldhauser, ya ce an samu karuwar fashin jirgi a watan da ya gabata.

Ya ce tun bayan shekarar 2011, an samu raguwar fashin saboda yawan sintirin da sojojin ruwa ke yi, da ma kara matakan tsaro da kamfanonin jiragen ruwan suka yi.

Jami'in ya yi wannan jawabi ne a lokacin da sakataren harkokin tsaron Amurka, Jim Mattis ya ziyarci sansanin sojinsu da ke Djibouti.

Kasar Somalia dai na fama da matsanancin fari wanda ya yi sanadiyar mutuwar dabbobi kuma ya sa rijiyoyi da koguna suka kafe, kuma hakan ya sa aka kasa yin noma.

Labarai masu alaka