US: Trump ya nesanta alakarsa da Rasha

Shugaba Donald Trump ya ce ba bu alaka tsakaninsa da Rasha
Image caption Shugaba Donald Trump ya ce ba bu alaka tsakaninsa da Rasha

Shugaba Donald Trump na Amurka ya jaddada cewa ba bu alakar da ke tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da Rasha.

A wata hira da akayi da shi a gidan talbijin din kasar na NBC, Mr Trump ya ce ba bu wani abu tsakanin sa da Rasha,kuma ba wata huldar kasuwanci tsakaninsu.

Ya ce yana son binciken da ake yi a kan zargin huldar da ke tsakaninsu, ayi shi yadda yakamata kuma cikin hanzari.

Kazalika Mr Trump, ya musanta cewa ya kori shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta kasar FBI, James Comey, ne saboda binciken da ya ke yi a kan zargin alakarsa da Rasha.

Shugaba Trump, ya ce ko da jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka ba su bayar da shawarar a sauke shugaban hukumar bincike ta FBI, James Comey ba, shi da kansa zai sallame shi daga aiki.

Saboda a cewarsa, Mista Comey mutum ne mai neman suna kawai, kuma hukumar ta FBI ta kasance cikin rudani.

Labarai masu alaka