Cutar yoyon fitsari: 'Sai ta ɓaci ake zuwa asibiti'

Masu cutar yoyon fitsari
Image caption Har yanzu akwai sauran aiki game da yaki da cutar yoyon fitsari a Nijeriya in ji wasu kwararru

Masana harkokin lafiya a Nijeriya sun ce ana samun adadin masu fama da cutar yoyon fitsari a ƙasar sakamakon dalilai da dama ciki har da "mummunar fahimtar da ake da ita game da zuwa asibiti".

Wani ƙwararren likitan masu yoyon fitsari, Dr. Adamu Isa al'umma a arewacin ƙasar na ganin zuwa asibiti ga masu larura ciki har da naƙuda "sai ta ɓaci".

Ya ce alƙaluma sun nuna duk shekara ana samun mata kimanin 12,000 zuwa 15,000 wani lokaci har 20,000 ma, da ke samun cutar yoyon fitsari.

Likitan na wannan jawabi ne a wani ɓangare na tunawa da ranar masu larurar yoyon fitsari, wadda Hukumar lafiya ta ware duk 23 ga watan Mayu don jimanta halin da suke ciki a faɗin duniya.

A cewar Dr. Adamu matsalar ta ta'azzara ne saboda rashin wadatar asibitoci ta yadda za su iya biyan buƙatun al'umma.

"Idan ka shiga karkara ka yi (tafiyar) kilomita 30 ko 50 daga cikin kowanne babban gari a Nijeriya, to idan ka je za ka ga asibitocin nasu kamar ba sa aiki.... Da ƙyar za ka samu likita ɗaya ko biyu."

Likitan ya ce lallai matsalar ta fi ƙamari a ƙauyuka inda ake fama da rashi (talauci), kuma babu cikakken ilmi. Babu hanyoyi.

Dr. Adamu Isah ya ce a baya-bayan nan hankalin hukumomi ya fara komawa yankunan karkara inda suka ɓullo da 'shirin kula da lafiya a matakin farko ƙarƙashin inuwa ɗaya'.

A cewarsa har yanzu wasu jihohin a arewacin Nijeriya ba su fara aiwatar da wannan shiri ba, duk da alfanun da yake ganin zai yi wajen rage cutuka irinsu yoyon fitsari.

Shi ma Dr. Umar Nasiru Ibrahim, shugaban asibitin masu yoyon fitsari na tarayya da ke Ningi a jihar Bauchi, ɗaya daga cikin manyan asibiti uku na musammam da gwamnatin Nijeriya ta bude don maganin cutar ya ce yoyon fitsari na da alaƙa da jahilci.

"Idan mace ta samu ciki, ta je inda za a kula da ita sosai, kuma aka gane cewa za a samu matsala, ba lallai ne a samu ciwon yoyon fitsari ba, matuƙar aka ɗauki matakan da suka dace."

Ya ce rashin daidaito tsakanin ɗan tayi a ciki da kuma ƙugun mace, ka iya janyo maƙalewar jariri a wajen haihuwa, kuma idan aka ɗauki dogon lokaci wani gefe ko dai na mafitsara ka iya zagwanyewa.

A cewarsa yoyon fitsari ka iya shafar hatta matan da suka daɗe suna haihuwa.

Ya ce: "Idan cikin da ta samu na gaba ya fi girman ƙugunta matuƙar ba ta samu kyakkyawar kulawa ba, kuma jaririn ya maƙale, tana iya samun yoyon fitsari."

"Haka ma a wajen haihuwar farko, idan yarinya ta yi ƙarama kuma ƙugunta bai gama girma ba, kuma jariri ya zo ya maƙale ba tare da an gano abin da wuri ba. Mafitsararta tana iya zagwanyewa."

Ya ce mafi yawan masu fama da larurar yoyon fitsari na zaune a gidajensu ba tare da sanin inda za su je a yi musu magani ba.

Dr. Umar Ibrahim ya ce sai a 'yan shekarun nan ne, gwamnatin Nijeriya ta buɗe asibiti uku manya don kula masu irin wannan cuta a faɗin ƙasar.

Labarai masu alaka