Amurka za ta sayar wa Qatar jiragen yaki

Jirgin yaki Hakkin mallakar hoto Huw Evans picture agency
Image caption Wasu kasashen kamar su Iran da Morocco da Turkiyya sun aika abinci kasar Qatar

Kasar Amurka ta amince ta sayar wa da Qatar jiragen yakin da kudinsu ya kai dala biliyan 12.

Hakan na zuwa ne a yayin da makwabtan Qatar suka mayar da ita saniyar ware, bisa zargin taimaka wa kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurkar za ta sayar wa da Qatar din jiragen yaki kirar F-15 da kudinsu ya kai dala biliyan 12.

A 'yan makonnin da suka wuce ne dai Amurkar ta amince ta sayar wa da Saudiyya makaman da kudinsu ya kai dala biliyan 100.

Kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE da kuma Masar sun yanke hulda da Qatar tare da rufe iyakokinsu ta sama da kasa da kuma ta ruwa.

Lamarin da shugaban Amurka Donald Trump ya goyi baya, yana mai cewa hakan ya biyo bayan mastin lambar da ya bukaci a yi wa masu taimaka wa kungiyoyin 'yan ta'adda.

Qatar dai ta musanta zargin da ake yi mata.

Labarai masu alaka