Me ya sa matan Boko Haram ke son komawa wurinsu?

Aisha, wata matar Boko Haram Hakkin mallakar hoto ADAOBI TRICIA NWAUBANI
Image caption Mijin Aisha, wanda kwamanda ne a kungiyar Boko Haram, ya yi ta bata toshin kayayyaki masu tsada

A jerin wasikun da ake aiko mana daga nahiyar Afirka, Adaobi Tricia Nwaubani, wadda'yar jarida ce ta duba yadda matan da dakarun Najeriya suka ceto ke komawa ga masu tsattsauran ra'ayin da suka sace su.

Bayan an samu labarin cewa wasu 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014 sun ki komowa ga iyayensu tare da wasu 82 da aka ceto a watan Mayu, duniya ta yi matukar mamakin wannan abin.

Hatta wani faifan bidiyo ya nuna 'yan matan, sanye da hijabai, kuma dauke da makamai suna cewa ba za su koma gida ba, duniya ta gasgata batun mai ban mamaki, inda wasu suke ta cewa: "Ta yiwu an dai tirsasa su ne kawai."

Har ila yau, wasu cewa suke "ba su iya gane abin da ya sa wata mace za ta so ta kasance da miyagun maza ba.''

Haka zalika, akwai wasu matan da sojojin Najeriya suka ceto da ke komawa dajin Sambisa, bisa radin kansu - Sambisa ita ce maboyar mayakan Boko Haram din da suka sace su tun farko, wato a arewa maso gabashin Najeriya.

'Rayuwar tatsuniya'

A watan Junairu, na gana da Aisha Yerima, mai shekara 25, wacce Boko Haram suka sace fiye da shekara hudu da ta gabata.

A lokacin da take hannun mayakan, ta auri wani babban kwamandansu, wanda ya nuna mata kauna sosai, tare da bayar da toshin kayayyaki masu tsada, har da rera mata wakoki yake da harshen Larabci.

Labarin da ta ba ni kan rayuwar Sambisa, tamkar wata tatsuniya na ji, kafin dirar da sojojin Najeriya suka musu yayin da mijinta ya fita yaki da sauran kwamandojin kungiyar.

A hirarmu ta farko da Aisha, tana hannun gwamnati har tsawon wata takwas, domin a sake mata tunani kan akidar da aka cusa mata, cikin wani shiri da wata likitar kwakwalwa Fatima Akilu ke gudanarwa, karkashin gidauniyarta Neem.

Aisha ta ce min, "Yanzu na gane cewa duk abubuwan da Boko Haram ke gaya mana karya ce kawai."

Ta kara da cewa, "Yanzu idan na ji su a rediyo sai kawai in yi dariya."

'Giyar Mulki'

A watan Mayu, kasa da mako biyar bayan sojoji sun mayar da ita hannun iyayenta a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriyar, sai ta koma maboyar Boko Haram din.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sojojin Najeriya ta fara fafatawa da kungiyar Boko Haram a shekarar 2009

Dokta Fatima ta shafe shekara biyar tana aiki da 'yan kungiyar Boko Haram, ciki har da yaransu da matansu da kwamandojin kungiyar, da daruruwan mata da aka ceto daga hannunsu.

Dokta Fatima ta ce, "yanayin da ko wace macce ta samu kanta a hannun Boko Haram, ya danganta ne da irin sansanin da ta tsinci kanta a ciki."

Ta kara da cewa, "Wadanda ke samun kula mai kyau, su ne wadanda suka amince da auren 'yan kungiyar, ko kuwa sun shiga ne da kansu, amma kuma irin su ba su da yawa, domin yawancinsu ana yi musu ne kamar yadda ake yi wa kowa."

Aisha ta bayyana mini yawan bayin da take da su a lokacin da take dajin Sambisa, da kuma daukakar da ta samu a hannun kwamandojin kungiyar, haka kuma irin yadda ta mallaki mijinta.

A cewar Aisha, har ta taba yi masa rakiya zuwa yaki sau daya.

"Yawancin ire-iren wadannan mata ba su taba wani aiki ba a rayuwarsu, ba su da wata daraja tsakanin al'ummarsu, sai kawai kwatsam ya zamana suna da iko da mata sama da 30 har zuwa 100 da ke mana bauta," in ji Dokta Fatima.

A cewar Dokta Fatima, abin da ya sa ke nan matan ba su iya zama idan an ceto su, saboda ba za su iya samun wannan ikon tsakanin al'ummarsu.

'Yanayin kaduwa'

Baya ga tube rigar mulki, a cewar Dokta Fatima, babban abin da ya sa matan ke komawa wajen Boko Haram shi ne wariya da kyama da suke fuskanta a tsakanin al'umma, wadanda ke tsangwamarsu saboda alakarsu da kungiyar, inda suke shigar da su cikin wani yanayi na kuncin rayuwa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu iyayen na fama da takaicin sace 'ya'yan nasu har yanzu

Dokta Fatima ta ce, "Akwai batun cire musu tsattsaurar akidar da aka cusa masu, a daya bangaren kuma shi ne samar masu karbuwa kuma tsakanin 'yan uwansu. Wasun su ba su da wata madogara a rayuwa."

Ta kara da cewa, "Irin tsarin taimakon cire akidar da ake yi baya binsu idan sun bar hannun mu. Sai su yi nasara samun lafiya a shirin na mu, amma da zarar sun koma gida, sai su shiga wani kangin rayuwa tsakanin al'ummarsu."

Adaobi ta ce, kwanan nan na kai wa 'yan uwan Aisha ziyara, wadanda har a wannan lokacin ke cikin kaduwa, saboda tafiyar ta, kuma suna cikin damuwa game da halin da take ciki.

Mahaifiyarta mai suna Ashe, ta ce ta tuna da wasu 'yan mata da Boko Haram suka aura, da suka koma hannun mayakan a dajin Sambisa, da dadewa kafin Aishar, ta kuma san wasu daga cikinsu.

Ashe ta ce, "Duk sanda daya daga cikinsu ta bace, sai iyayenta su zo wajen Aisha suna tambayarta ko ta ji daga garesu," ta ce "Ta haka ne na sani."

Wasu daga cikin 'yan matan sun ci gaba da yin waya da Aisha, ko bayan komawarsu hannun Boko Haram, inda kanwarta Bintu ma ta ce sau biyu tana shaida hakan.

Rayuwa ta cigaba

Ba kamar sauran matan Boko Haram din da na hadu da su ba, da ke fama da mummunar yanayin rayuwa cikin tsangwama da kyama, Aisha ta samu ni'ima wajen ci gaba da rayuwarta.

Ta kama sana'ar kasuwancin atamfofi, kuma tana yawan zuwa bukukuwa inda take yawan wallafa hotunan ta a shafukan sada zumunta, inda take kurewa adaka, kuma take samun masu kyasawa da dama.

"Akalla mutane biyar ne suka neme ta da aure," in ji mahaifiyar Aisha, inda ta jaddada cewa babu abin da ya fi hakan nuna samun karbuwa tsakanin al'umma, haka kuma a cewarta hakan ya tabbatar da cewa diyarta ba ta fuskanci wata tsangwama ba.

"Daya daga cikin masoyan nata ma mazaunin Legas ne, kuma har tana tunanin aurensa," in ji Aisha.

Amma kuma duk komai sai ya watse, bayan da ta ji labarin cewa mijinta dan Boko Haram ya auri wata mata da suke kishi da ita.

Daga nan ne Aisha ta yi tutsu, ita da aka sani da shiga jama'a, sai ta koma tana boye kanta.

Kanwar ta Bintu ta ce, ta koma ba cin abinci, ba magana, sai kullum ta zauna cikin kunci.

Bayan makwanni biyu ta gudu daga gida, da wasu 'yan kayayyakin ta.

Aisha ta kashe wayoyinta, ta kuma dauki dan ta namiji da ta haifa tare da mijinta kwamandan Boko Haram, a dajin Sambisa, amma kuma ta bar babbar diyarta mace da ta haifa tare da tsohon mijinta, kafin Boko Haram su sace ta.

Cire masu akidar tsattsaurar ra'ayi na da sarkakiya, saboda har yanzu ana fama da tarzomar.

"An fi samun sauki idan har aka samu daidaito tsakanin kungiyoyin ta'addan da gwamnatin kasar, inda har suka amince da su mika wuya su ajiye makamai." in ji Dokta Fatima.

Ta akara da cewa."Matsaslar idan akwai iyaye ko mazaje da 'ya'ya maza da ke ci gaba da rikicin, to sai ka ga suna bukatar komowa da iyalansu, musamman matansu."

Asta, wata matar 'yan Boko Haram ce, kuma ta shaida min cewa yawancin matan na komawa ga kungiyar, amma ita ba ta da bukatar yin haka.

Amma 'yar shekara 19 da ta bayyana min yadda take matukar kewar mijinta, da kuma yadda take bukatar shi da kuma komawa a gareshi.

Amma kuma ta ce ita ba za ta koma dajin Sambisa ba, ko da an bukace ta da hakan, sai dai ya zo su zauna tsakanin al'umma tare.

Sai dai kamar Aisha, akwai yiwuwar bukatar ganin mijin nata ya mamaye tunaninta, har ya sha gaban cewa kungiyar ce ke da alhakin dubban mutane da suka rasa rayukansu a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma rasa muhallan miliyoyi, haka kuma a yanzu suka jefa wasu dama cikin mummunar hali a sansanonin 'yan gudun hijira.

Hakkin mallakar hoto ADAOBI TRICIA NWAUBANI
Image caption Adaobi Tricia Nwaubani ce 'yar jaridar da ta yi wannan bincike

Labarai masu alaka