Kenya: Raila Odinga zai nufi kotu

Raila Odinga Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan takarar da ya sha kaye a zaben shugaban kasar Kenya, Raila Odinga, ya bayyana cewa zai nufi kotun kolin kasar domin kalubalantar zaben da aka gudanar a makon jiya.

Mista Odinga ya ce gamayyar jam'iyyun adawa, NASA, sun kammala tattara bayanan abin da ya kira "gagarumin magudin zabe" da aka yi.

A baya ya taba cewa ba zai dauki wannan matakin ba.

Amma masu sa ido na kasa da kasa sun bayyana zaben a mai inganci kuma wanda aka yi adalci.

A wani labarin, gwamnatin Kenya ta dage shawararta ta dakatar da wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama wadanda suka nuna rashin gamsuwa da sahihancin zaben.

Wannan matakin ya biyo bayan wani samame da jami'an 'yan sanda da na haraji suka kai a ofishin daya daga cikin kungiyoyin.

Labarai masu alaka