Wasu 'yan Boko Haram sun mika wuya a Nijar

Ba wannan ne karon farko da 'yan Boko Haram suka mika wuya a jamhuriyar Nijar ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da 'yan Boko Haram suka mika wuya a jamhuriyar Nijar ba

'Yan kungiyar Boko Haram da dama sun mika wuya ga hukumomin jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijar, inda aka kai su wani waje na sirri aka ajiyesu.

Gwamnan jihar Diffa, Lawwali Mahaman Dandano, ne ya bayyana hakan, amma kuma bai sanar da adadin mutanen ba.

Gwamnan ya ce, yanzu haka mutanen da suka mika wuyan, suna nan ana kula da su da kuma ba su tarbiyya bakin gwargwado.

Lawwali Mahaman Dandano, ya ce nan gaba kadan za a ba wa mutanen horo a kan sana'oi daban daban, inda da sun kammala za a ba su aikin yi, sannan a kai su wajen iyalansu.

Daga nan gwamnan, ya yi kira ga sauran 'yan Boko Haram din da ke son mika wuya, amma suna tsoro, da su zo, domin ba duka ba zagi, za a karbe su hannu bibbiyu.

Ba wannan ne karon farko da 'yan Boko Haram din suka mika wuya a jamhuriyar Nijar ba.

Labarai masu alaka