Facebook zai fallasa bayanan kutsen zaben Amurka

Mark Zuckerberg Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya ce kamfanin nasa zai mika wa majalisar Dattijan Amurka bayanan tallace-tallace 3,000 da aka alakanta su da kasar Rasha dangane da zaben shugaban Amurka.

Mista Zuckerberg ya sha alwashin baza komai a faifai daga yanzu dangane da labaran karya da aka rika yadawa a Facebook.

A farkon wannan watan ne aka gane cewa kamfanin Facebook ya gudanar da bincike dangane da tallan siyasa da kasar Rasha ta dauki nauyi - tuhumar da Rasha ta musanta.

Bayan fuskantar matsi daga jama'a, kamfanin Facebook ya yarda ya mika wadannan tallace-tallacen ga wani kwamitin majalisar Dattijan Amurka dake binciken kutsen da Rasha tayi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen shekarar 2016.

A cikin jawabin da yayi mai tsawon minti 9, Mista Zuckerberg ya ce shafin na Facebook zai rika fayyace wa masu amgfni da shafin inda kudaden tallan da ake saka wa suka fito.

Mista Zuckerberg ya ce: "Bayan bayyana sunan shafin da ya biya kudin tallan da kake da sha'awar sani, zamu kuma ba kowa damar ziyartar ainihin shafin da ya saka tallan domin ganin dukkan tallace-tallacen da ya saka a Facebook."

Kamfanin ya ce yana da shirin amfanin da kwararru wajen tantance irin wadannan tallace-tallacen. Amma ana jin zai yi matukar wahala ganin girman aikin dake gabansa, inji Siva Vaidhyanathan, wani farfesan ilimin sadarwa dake jami'ar Virginia:

"A ganina kamar ba shi da iko a kan wannan tsarin da ya gina da hannunsa, Kamfanin Facebook ba zai iya daukan isassun ma'aikatan da zasu rika sayar wa wasu mutane guraben talla ba. A ganina tsarin na Facebook shi ne matsala", inji Farfesa Siva.