Ana zubar da ciki sau miliyan 56 a duniya duk shekara - WHO

Wata mata na shan fama da azabar ciwon mara sakamakon zubar da ciki da tay a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata na shan fama da azabar ciwon mara sakamakon zubar da ciki da tay a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ce kashi 50 cikin 100 na zubar da ciki da ake yi a duniya na cike da hadari.

Jaridar Guardian ta Birtaniya ta ambato wani rahoto na wani bincike da hukumar WHO ta gudanar, wanda ya nuna cewa ko wacce shekara ana zubar da ciki kusan sau miliyan 56 a fadin duniya, kuma kusan rabi na cike da hadari.

Yawan zubar da ciki da ake yi mai cike da hadari na faruwa ne a Afrika, inda zubar da ciki daya cikin hudu ne kawai ba ya zuwa da hadari, kuma a nan ne aka fi samun yawan mace-mace sakamakon zubar da cikin.

A cikin wani bincike da aka wallafa a wata mujallar lafiya ta Lancet, ya ce an zubar da ciki sau miliyan 55.7 a ko wacce shekara daga 2010 zuwa 2014 a duniya.

Binciken ya kuma ce miliyan 17.1 na cikin da aka zubar ya zo da hadari, saboda matan da suka aikata haka din sun sha magunguna ne da kansu ko kuma wasu kwararru sun taimaka musu amma ba ta ingantacciyar hanyar da ta dace ba.

Labarai masu alaka