Falasdinawa: Amurka da Isra'ila za su fice daga UNESCO

Amurka ta ce dalilai biyu ne suka sa ta yanke shawarar ficewa daga UNESCO
Image caption Amurka ta ce dalilai biyu ne suka sa ta yanke shawarar ficewa daga UNESCO

Kasashen Amurka da Isra'ila sun sanar da ficewarsu daga hukumar bunkasa ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, saboda abinda su ka kira kin jinin da take nunawa Isra'ila.

Ma'aikatar hulda da kasashen wajen Amurka ta ce abinda ya kara mata kaimin ficewa shi ne dimbin bashin da UNESCO ke bin kasar, bayan da ta dakatar da ba da kudin tallafi shekaru shida da suka wuce saboda karbar wakilcin Falasdinawa da hukumar ta yi.

Firayiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana matakin na Amurka a matsayin wani abin jarumta da kuma kare mutunci.

Shugabar UNESCO, Irina Bokova ta ce ba ta ji dadin matakin ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, janyewar za ta kankama a karshen shekara mai zuwa.

Labarai masu alaka