Iran: Ana zaman makoki bayan mutuwar mutum 400

Rugujiwar gidaje a girgizar kasa a Iran
Image caption An kaddamar da gagarumin aikin ceto

Bayan girgizar kasar da ya sanadiyar mutuwar mutum sama da 400 a Iran, gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar makoki a duk fadin kasar.

Masu ceto sun shafe dare baki daya su na neman masu sauren shan ruwa a gaba da suka makale a cikin tarkace.

Duban 'yan kasar Iran da dama ne suke kwashe dare na biyu a fili Allah ta'ala, wato ba cikin mahalansu ba.

Sun kwashe daren na biyu a wani yanayi na iska mai sanhi da ke ke kadawa.

A kalla mutum sama da 400 ne suka mutu kuma wasu kusa 700 suka samu raunika daban -daban, sanadiyar girgizar kasar ta ranar lahadi.

Har dai cikin dari, masu cuto na ci gaba da neman mutanan da suka makkale a cikin tarkace a yankin gabashin kasar,musamman a yakin Kermanshah mai tsauni .

Gwamnati kasar ta Iran dai ta sanar da cewa wannan rana ta Talata, za ta kasance ranar makoki a cikin kasar baki daya.

Labarai masu alaka