Trump zai ayyana Kudus a matsayin babban birnin Israila

Shugaba Trump ya ce zai umarci ma'aikatar harkokin wajen kasarsa da ta fara kokarin mayar da ofishin jakadancinsu zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump ya ce zai umarci ma'aikatar harkokin wajen kasarsa da ta fara kokarin mayar da ofishin jakadancinsu zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv

Shugaba Tump na da aniyyar ganin ya cika alkawarin da ya yi wa masu goyon bayan Israila a lokacin yakin neman zabe, amma yayin wannan ya tabo daya cikin batutuwa masu zafi a rikicin da ke tsakanin Israila da Palasdinu wato makomar birnin Kudus.

Shugaba Trump ya kira wasu shugabannin kasashen Larabawa ta wayar tarho a ranar Talata, domin ya fada musu aniyarsa ta mayar da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel aviv zuwa birnin Kudus.

Ya kuma ce zai umarci ma'aikatar harkokin wajen kasarsa da ta fara kokarin mayar da ofishin jakadancinsu zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv.

Sai dai Sarki Salman na Saudiyya ya fada masa cewa duk wani yunkuri irin wannan zai harzuka musulmi a kasashen duniya.

Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan duk wani mataki da ka iya kawo nakasu a kokarin da ake wajen ganin an cimma maslaha tsakanin Israila da Palasdinu.

Amma tun farko mai magana da yawun fadar White House Sarah Sanders, ta ce Shugaba Trump ya ce zai ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin idan ya dauki wannan mataki.

Isra'ila dai ta dauki birnin Kudus a matsayin babban birinin kasar, yayin da Falasdinu sun ayyana gabashin Kudus a matsayin wurin da zai kasance babban birninsu idan sun kafa tasu kasar.

Idan Amurka ta amince da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, toh za ta kasance kasa ta farko da za ta yi haka tun bayan kafuwar Israilar a shekarar 1948.

Labarai masu alaka