Mutum sama da 20 sun mutu a Niger sanadiyar sankarau

Shugaban jumhuriyar Niger
Image caption Mahamadou Issoufou

A jumhuriyar Niger kamar a sauren kauyukan na Afirka al'umma na fama da karamcin gidajen assibiti.

Wannan kuma na daya daga cikin abubuwan more rayuwa da yawancin mazauna karkara ke kokawa game da rashin samunsu.

Al'ummar kauyen Unguwar Garin Mallam, ajihar Mirriyan da ke yankin Damagaram a jumhuriyar Niger na fuskantar irin wannan matsala.

Kauyen na kunshe da al'ummar da yawanta ya kai 6,000.

Image caption Mahamadou Issoufou

An kiyasta cewa kawo yanzu cutar sankarau da ta barke a kauyen ta kashe mutane sama da 20.

Da dama daga cikin mazauna kauyen maza da mata , na ganin rashin asibiti ko dakin shan magani ya ta'azzara matsalar.

Mata masu juna biyu na galabaita kan hanyar su zuwa assibiti mafi kusa da ke da nisan kilomita takwas da kauyen.

Al'ummar dai sun yi kira ga gwamnatin da ta samar masu da assibiti domin kawar da matsalolin rashin lafiyar da su ke fuskanta.

Labarai masu alaka