Barbara Bush matar tsohon shugaban kasar Amurka ta mutu

Barbara ita ce matar George Bush Babba, kuma uwar Bush karami Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barbara ita ce matar George Bush Babba, kuma uwar Bush karami

Barbara Bush, matar tsohon shugaban kasar Amurka, ta rasu tana da shekaru 92.

Barbara, matar George Bush Babba, kuma uwar Bush karami, ita kadai ce matar da aka rantsar da mijinta da danta a idonta a matsayin shugabannin kasa a Amurka.

Misis Bush ta sha fama da rashin lafiya na dan wani lokaci, kafin a cikin karshen mako a sanar da cewa ba ta bukatar kulawar asibiti.

A zamaninta a fadar White House a farkon shekarar 1990 zuwa 2000, ayyukanta sun wuce na matar dan siyasa da aka sani a bisa al'ada.

Barbara ta kaddamar da gidauniyar ilimin iyali da ke bayar da taimako ga iyaye da yara.

Haka kuma ta sha nuna adawarta kan nuna bambanci da adawarta kan wasu manufofin mijinta a jami'iyyar Republican.

Labarai masu alaka