Kun san wanda zai gaji Arsene Wenger a Arsenal?

A shekarar 1996 aka nada Arsene Wenger a matsayin kocin Arsenal Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption A shekarar 1996 aka nada Arsene Wenger a matsayin kocin Arsenal

Su wane ne za su iya gadar Arsene Wenger bayan da ya sanar da cewa zai bar kungiyar a karshen kakar bana bayan shafe shekara 22 a kulob din.

Wenger, wanda aka nada a matsayin kocin Arsenal a watan Oktoban 1996.

Kocin haiffen kasar Faransa ya lashe gasar Premier uku da kofin FA sau bakwai.

Ya kafa tarihi inda ya zamo kocin farko a tahirin gasar da ya lashe Lig a kakar 2003/2004 ba tare da an doke shi ba.

Sai dai Wenger ya fuskanci kalubale a 'yan shekarun baya-bayan nan, inda ya ka sa ja da kungiyoyi irinsu Chelsea, Manchester City da tsohuwar abokiyar hamayyarsa Manchester United.

Kuma rabon da kulob din ya sake lashe gasar ta Premier tun wannan shekara, abin da ya sa wasu magoya bayan kungiyar da dama ke ta kiraye-kirayen ya tattara inasa-inasa ya kara gaba.

To ko wane ne zai iya maye gurbin kocin?

Ganin shekarun da Wenger ya shafe a Arsenal, da kuma irin rawar da ya taka, inda ya fito da manyan 'yan wasa da dama kamar su Thierry Henry, Patrick Viera, Ian Wright, Tony Adams, Robin Van Persie da dai sauransu, wasu na ganin da wuya a iya maye gurbinsa cikin sauki.

Patrick Viera

Image caption Patrick Vieira haifaffen kasar Senegal

Tsohon kyaftin din Arsenal ne wanda ya taka leda a karkashin Arsene Wenger.

Ya lashe kofuna da dama a kulob din.

Tsohon dan wasan na Faransa na da farin jini a tsakanin magoya bayan Arsenal sai dai komawar da ya yi Manchester City daga baya ta dan rage masa kima a idon wasunsu.

Yana da kwarewar aikin koci ganin cewa ya taba zama kocin tawagar matsan City, kuma a yanzu shi ne kocin New York City FC, wanda mallakar mutanen da suka mallaki City ne.

Thierry Henry

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Thierry Henry

Thierry Henry:

Shi ne mutumin da ya fi kowa zura kwallo a tarihin Arsenal, kuma ya lashe kufuna da dama a shekara takwas da ya shafe a kulob din.

A yanzu yana sharhi ne a gidan talbijin na Sky Sport.

Arsene Wenger ya so ya nadashi kocintawagar matsan Arsenal amma ba su daidai ta saboda ya ki yarda ya ajiye aikinsa na Sky Sportl

Don haka wasu na ganin ba lallai ba ne a bashi aikin a yanzu ganin cewa Wenger na iya taka rawa a wurin nada wanda zai gaje shi.

A yanzu shi ne mataimakin koci na biyu na tawagar kwallon kafa ta Belgium.

Mikel Arteta

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mikel Arteta

Tsohon kyaftin din Arsenal kuma dan kasar Spaniya.

Ya taka rawar gani sosai a kulob din kuma yana da dangantaka mai kyau da Arsene Wenger da sauran shugabannin kulob din.

A yanzu mataimakin kocin Manchester City ne Pep Guardiola.

Wasu na ganin zai dace da kocin Arsenal, yayin da wasu masu sharhi ke ganin ba shi da kwarewa sosai.

Kuma ba lallai ba ne ya so barin City a yanzu.

Joachim Low

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Joachim Low

Kocin twagar kwallon kafa ta kasarJamus, wanda ya lashe kofin duniya a Brazil a 2014.

Ya kuma lashe kofin nahiyoyi na 2017 a kasar Rasha.

Shi zai jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha, kuma wasu na ganin zai iya karbar aikin Arsenal bayan kammala gasar ta Rasha 2018.

Ya kware sosai kuma ya yi suna - wasu na ganin shi ne ya fi kowa dacewa da Arsenal ganin irin salon kwallon da yake buga wa da kuma tahirin kulob din karkashin Wenger.

Carlo Ancelotti

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlo Ancelotti

Tsohon kocin Bayern Munich, Real Madrdi, Chelsea, AC Milan, yana da kwarewa sosai ganin irin rawar da ya taka a baya da kuma kungiyoyin da ya horas.

Ya kuma taba aiki a Ingila.

Sai dai wasu na ganin ya fara tsufa kuma kwarewar ta fara raguwa idan aka yi la'akari da rawar da ya taka a Bayern Munich, inda aka sallame shi a farkon kakar bana.

Sannan wasu magoya bayan Arsenal na nuna shakku kan irin salon wasan da yake taka wa.

A yanzu dai za a zuba ido daga nan zuwa wani dan lokaci domin ganin irin hukuncin da mahukuntan Arsenal za su dauka.

Babu shakka kuma wannan shi ne babban abin da zai zauna a zukatan magoya bayan kungiyar da kuma masu sharhi kan al'amuran wasanni har zuwa lokacin da za a bayyana sunan wanda zai ga ji Arsene Wenger.

Kuma ko wane ne aka bai wa wannan mukami, to babu shakka zai gaji babban kalubale musamman ganin shekarun da Wenger ya shafe da kuma irin sauyin da ake samu a gasar Premier da ma kwallon kafa ba ki daya.