Yadda Real Madrid ta doke Leganes

Gareth Bale ya ci kwallonsa ta 15 a raga a kakar bana inda ya taimaka wa Real Madrid doke Leganes.

Zinedine Zidane ya yi sabon zubin 'yan wasa 10 bayan ga wadanda suka doke Bayern Munich a gasar zakarun Turai a Jamus.

Kocin ya ajiye Ronaldo domin gasar zakarun Turai.

Bale ne ya fara ci wa Madrid kwallo a ragar Laganes ana minti 8 da fara wasa, yayin da Mayoral ya ci kwallo ta biyu.

Laganes ta rama daya a kafar Brasanac bayan an dawo hutun rabin lokaci, yayin da aka ba dan wasanta Appelt Pires jan kati ana dab da hure wasa.

Yanzu maki daya ne ya raba Real Madrid da ke matsayi na uku da kuma Atletico Madrid da ke matsayi na biyu a teburin La liga.

Real yanzu za ta mayar da hankali ne a karawar da za ta yi da Bayern Munich a gasar zakarun Turai a ranar Talata.

Ga wasu hotunan yadda ta kaya a karawar Real Madrid da Leganes:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Labarai masu alaka