Damben Roget da Shagon Aleka
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Roget da Shagon Aleka

Wasu sakamakon wasannin da aka dambata a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Damben da aka yi kisa:

 • Dogon Sadauki daga Arewa ya buge Shagon Dangero Guramada.
 • Shagon Bahagon ba matsala Guramada ya yi nasara a kan Shagon Shamsu Kanin Emi daga Arewa.
 • Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya buge Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa.
 • Shagon Bahagon Dan Katsinawa daga Arewa ya buge Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu.

Wasannin da aka yi canjaras:

 • Shagon Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa.
 • Dogon Aleka daga Kudu da Garkuwan Dangero Guramada.
 • Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu da Bahagon Alin Tarara daga Arewa.
 • Autan Bahagon Maru daga Arewa da Shagon Idi Guramada.
 • Shagon Autan Faya daga Kudu da Autan Bahagon Maru daga Arewa.
 • Bahagon Audu Argungu daga Arewa da Autan Faya daga Kudu.
 • Dogon Bahagon Sisco daga Kudu da Autan Fafa daga Arewa,

Labarai masu alaka