BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 04 Disamba, 2009 - An wallafa a 11:29 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Makarantar Aikin Jarida - Horo a kan harshen turanci
 

 
 
Gabatarwa

Don a tabbatar da dorewa, inganci da daidaito a aikin jarida, harshe yana taka mahimmiyar rawa. Wadannan sabbin manhajojin zasu taimakawa manema labarai a kasashen duniya wajen bunkasa harshen turanci kamar yadda ayyukansu ke bukata.

Horo a kan harshen turanci a BBC zai taimakawa bukatun dinbim masu sauraro ko maaikatan dake aiki a fannoni daban daban na aikin jarida da shirye shirye . Zai taimakawa cigabansu ta fannin harshe a cikin gida da kasashen waje da kuma a fannoni daban daban.

Wadannan sabbin mahajoji da Mark Shea na cibiyar kasa da kasa, CoJo ya tsara, su ne irinsu na farko da za’a kaddamar a shafin intanet na makarantar aikin jarida.

Wannan ci gaba ne mai ban sha'awa da zai baiwa tawagar kwararrunmu a fannin harshen turanci da kuma masu bada horo su koyar da abinda suka sani wajen horad da 'yan jaridun BBC a duk fadin duniya da kuma masu neman sani a kan turanci a ko’ ina.

Muna fatar za ku ji dadin koyo tare da mu!

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri