Hotuna da Bidiyo – Tambayoyin Da Aka Saba Yi

Ta yaya zan kunna sauti / kalli bidiyo a waya tat a salula?

Domin sauraron sauti / kallon bidiyo, za a bukaci wayar salula da ta dace da yin hakan. Ana kuma bukatar saita layin wayar salula domin samun bayanai ta hanyar GPRS, WAP ko 3G. Domin samun Karin bayani, a tuntubi kamfani day a samar muku da layin wayar.

A wadanne tsare-tsaren zan samu wadannan bayanan?

Sauti:

  • Sauko da sauti(MP3)
  • Sauraro kai tsaye: 3GP, Windows Media, Real Media

Nawa zan kashe wajen yin hakan?

BBC ba ta cajin kudi domin kallo ko sauraren bidiyo ko sauti a shafinta. Sai dai kamfanin da ya samar maka da layin wayar salula zai iya cajar ka kudin adadin bayanai da ka sauko da su daga intanet.

Idan baka da tabbas kan yawan kudaden da za a caje ka dan yin amfani da yanar sadarwa a wayar salularka, tuntubi wadanda suka samar maka da layin waya.

Wanne tsawon lokaci zai dauke ni wajen sauko da abu daga intanet?

Hakan ya danganta ne da surin intanet dinka. A yanyi da ya dace dai, za a iya sauko da kowanne irin fayil daga intanet cikin kasa da mintuna biyu.

Ta yaya zan saurari sauti / kalli bidiyo?

Zabi abin da kake so ka kalla, sai ka latsa inda aka rubuta sauko da sauti / bidiyo, kuma da zarar an kammala sauko da shi, abin zai kunnu nan take a cikin garmahon wayar salularka.

A wasu lokutan za ka bukaci nemo fayil din da ka sauko da sauti / bidiyon a cikinsa domin kunna wa daga can. Muna maraba da tsokaci da kuma shawarwarinku a kan aikin samar da bidiyon nan. Sai ku tuntube mu a hausa@bbc.co.uk.