Taimako

Ta yaya zan adana shafin wayar Salula na BBC?

Adanawa zata ajiye maka shafukan yanar sadarwa da kake sha'awa, ta yadda zaka same su duk lokacin da kake bukata. Idan zaka yi amfani da shafin wayar salula na BBC, zaka iya yin haka ta hanyar "adanawa" (bookmark", ko "kara adanawa" "add bookmark)" ko kuma ta bangaren "shafukan da kake sha'awa" (favourites).

Nan gaba idan zaka shiga shafin wayar salula na BBC a yanar gizo, abinda zaka yi shi ne ka tafi kai tsaye zuwa bangaren "adanawa/ ko shafukan da kake sha'awa" (‘Bookmarks'/Favourites'). Domin neman tallafi kan yadda zaka adana shafin salula na BBC, tuntubi kundin bayanai na wayar salular ka, wato user manual.

Me nene adireshin shafin yanar sadarwa na wayar salula na BBC?

http://www.bbc.co.uk/hausa/mobile

Zaka iya adana wannan adireshi a bangaren "adanawa /ko kuma shafukan da kake sha'awa", ta yarda ba sai ka sake rubutawa ba duk lokacin da zaka ziyarci shafin nan gaba.

Nawa ake kashewa idan za a yi amfani da shafin sadarwa na wayar salula ta BBC?

BBC bata karbar kudi domin baka damar shiga shafinta na yanar sadarwa a wayar salula. Sai dai kamfanin dake samar da layin wayar ka zai iya cazar ka gwargwardon yawan shafukan sadarwar da ka shiga. Idan kana son sanin yawan kudin da za a caje ka idan kai amfani da shafukan sadarwa ta wayar salula, zaka iya tuntubar wadanda suka samar maka da layi domin karin bayani.

Yadda za a iya rage kashe kudi:

  • Akwai hanyoyi da dama da za a iya rage kashe kudi idan mutum yana zagayawa (browsing) a shafukan sadarwa ta wayar salula. Samun bandir na shafukan sadarwa (data bundle). Za a iya sayen gurbi na shafukan sadarwa a dunkule na wata-wata ko kuma kowacce rana. Hakan zai rage yawan kudaden da zaka kashe a wata wajen zirga zirga a shafukan sadarwa musamman idan kana yawan amfani da yanar sadarwa. Domin karin bayani tuntubi kamfanin da ya samar maka da layi.
  • Yin amfani da na'urar sadarwa ta wayar iska(Wi-Fi). Wayar salula da dama a yanzu tana zuwa da na'urar sadarwa ta wayar iska a cikinta. Ta wannan hanyar zaka iya rage kudin da kake kashewa idan kana ziyartar shafin sadarwar wayar salula na BBC Hausa, ta yin amfani da hadi na wayar iska, a gida ko a inda ake amfani da wayar iska. Idan baka da tabbas ko wayar ka tana dauke da na'urar sadarwa ta wayar iska, tuntubi kamfanin da ya kera wayar salular ka, ko kuma kamfanin da yake samar maka da layin sadarwa.

Ta yaya zan iya tuntubar BBC?

Muna maraba da ra'ayoyinku kan shafukan yanar sadarwar na wayar salula da muke samarwa. Sai dai muna so a fahimci cewa ba zamu iya amsa dukkan ra'ayoyin da kuka aiko mana ba. Zaku iya aiko mana da bayanai, tambayoyi ko shawarwari ta email: hausa@bbc.co.uk sai dai ya kamata a fahimci cewa wannan email na samun ra'ayoyi ne kawai kan samarda shafukan sadarwa a wayar salula na BBC Hausa.

Menene matsayin BBC kan makala shafukan sadarwa na waje a nata shafin?

Idan muka ga ya dace da sharuda na aikin jarida, http://www.bbc.co.uk/hausa/mobile shafin yanar sadarwar mu na iya makala wasu shafukan da suke wajen BBC.

Ba ma makala adireshin wasu shafukan yanar sadarwa domin neman kudi ko kuma wata bukata. Dukkan shafukan da muka makala http://www.bbc.co.uk/hausa/mobile mun yi haka ne bayan mun gamsu da cewa sun cika wasu sharuda sannan kuma masu sauraren mu zasu bukace su.

BBC ba zata dauki alhakin bayanan da shafukan waje da ta makala a adireshinta na yanar sadarwa suka kunsa ba, duk da cewa an yi nazari akansu gwargwadon sharudan aikin jarida na BBC. Ya kamata a fahimci cewa saka shafuka daga wajen BBC, ba yana nufin BBC ta amince da shafin bane kacokam.

BBC tana maraba da ra'ayoyin ku kan dacewar shafukan sadarwar da ta makala a adireshinta. Idan kuna bukatar yin tsokaci, sai ku tuntube mu.

Yaya zan iya samun karin bayani kan shafukan yanar sadarwa na wayar salula na BBC?

Latsa wannan adireshin domin karin bayani a harshen turanci kan ka'idojin yin amfani da kuma manufofin kiyaye bayanai:

Terms of Use and Conditions Privacy Policy