BBC navigation

Widget na BBC

Menene Widget na BBC?

Widget na baka damar ka kwashi bayanani daga shafin intanet na BBC ka kuma sake amfani da su a wani shafin intanet din, ko kuma zuba bayanan a cikin kwamfiyutarka.

Widget din BBC Hausa zai baka damar ka sanya labarai da rahotannin BBC, da murya da ma bidiyo a shafinka na intanet.

Me ya sa zan bukaci Widget din BBC?

Ta hanyar amfani da Widget din BBC Hausa, za ka iya sanya labarai da rahotanni daga sassa daban daban na duniya a shafinka na intanet domin masu ziyartar shafinka su amfana. Hanya ce mai sauki ta samar da bayanai ga masu ziyarar shafinka cikin sauki.

Ta yaya zan sanya Widget din BBC a shafi na?

Abu ne mai sauki, kawai ka kwafi rubutun da ke sama, ka sanya a shafinka na intanet.


Akwai Karin wasu samfurin na Widget ga masu amfani da iGoogle, Windows Vista Sidebar, Netvibes, Mac Dashboard da WordPress. Sannan nan gaba za a samu kari.

Yadda Widget din BBC zai bayyana a shafinka

Labarai na baya-bayan nan


Latsa “abin da shafi ya kunsa” domin ganin abubuwan da ake da su na widget. Masu amfani da shafi za su iya zabar nauin bayanan da suke sha’awa.

Binciki shafin BBC Hausa

Masu amfani da shafinka za su iya amfani da widget din wajen bincika labaran BBC Hausa.

Kawai ka rubuta kalma ko jimla a cikin gurbin bincike, kuma Widget zai kai ka zuwa sakamakon binciken da kake nema.

Samu wannan Widget din

Masu ziyartar shafinka su ma za su iya samun widget din domin shafinsu na intanet ta hanyar latsa maballin + .

Wannan zai bayyana rubutun da ake bukata na sanya widget a shafi.

Zabi

Ga wasu daga cikin zabin da ke akwai ga masu ziyartar shafinka. Sauya wannan zabin, zai shafi yadda Widget din zai bayyana a shafinka ga masu ziyartarsa.

Zabi bayanan da kake son samu

Zabi bayanan da kake son su fara bayyana a duk lokacin da aka sanya widget.

Boye takaitattun bayanai

Ka sanya alama a cikin akwatin don nuna taken labari, ba tare da takaitaccen labarin ba.

Boye hoto

Ka sanya alama a cikin akwati domin boye hotuna.

Taimako

Ka latsa alamar tambaya don kai ka shafin taimako.

Martani da kuma tambayoyi

Za mu so mu ji ra’ayinka dangane da wannan. Me ya baka sha’awa, me kuma kake son a inganta?

Ka’aidojin amfani da Wiget

Ta hanyar sanya bayanan Widget din BBC a shafinka, da kuma amfani da shi wajen sanya bayanai daga shafin BBC a shafinka, ka amince kenan da ka’idojin da aka bayyana a kasa.

1. Lasisi

1.1 BBC ta baka cikakkiyar dammar amfani da widget dinta don sanya bayanan shafin BBC a shafinka.

1.2 Duk wasu hakkoki, da hakkin mallaka na widget din BBC Hausa, mallakin BBC ne.


2. Amfani da widget din BBC da kuma bayanan BBC.

2.2 Widget din BBC don amfanin kai ne kawai, ba don harkar kasuwanci ba.

2.3 Ba a baka damar kwafa, sake wallafawa, yin sauyi, ko kuma yin kari a cikin bayanan widget din BBC ba, kuma ba ya halatta ka hada Widget din BBC da wasu bayanai.

2.4 Bai halatta ka kwafa, rarraba ko kuma sauya yanayin Widget din BBC ba ta kowacce fuska.

3. Rashin Alhaki

3.1 BBC tana samar da Widget dinta ne a duk lokacin da ya samu, kai kuma ka sauko da shi, ka kuma sanya a shafinka, bisa radin kanka.

3.2 BBC ta yi kokari wajen tabbatar da cewa, Widget dinta da bayanan da ya kunsa ba su dauke da kura kurai, ko illa. Sai dai BBC ba ta da alhaki idan hakan ta kasance.

3.3 A iya yadda doka ta tanada, BBC ba za ta dauki duk wani alhaki ba, idan sakamakon amfani da Widget dinta wani abu ko illa ta samu ga shafinka na intanet.

3.4 Ana shawartarka da ka dauki dukkan matakan da suka kamata, domin kare kwamfiyutarka daga duk wata illa da virus ka iya yi mata.

3.5 BBC za ta iya sauya wa, ko kuma cire bayanan dake cikin Widget dinta a duk lokacin da take so, kuma za ta iya toshe ka daga amfani da widget dinta idan ka saba wa wadannan ka’idojin.

4. Gamewa

4.1 Wadannan ka’idojin za a fassara su ne bisa dokokin kasar Ingila kuma bisa hurumin kotunan yankin Ingilishi.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.