Shiga Gasar nuna basira ta BBC

Global Creative Challenge

Sashen watsa shirye shirye ga duniya na BBC, ya hada guiwa da hadaddiyar kungiyar matasa masu basira ta YCN domin kaddamar da ''Gasar nuna basira ta duniya''.

Manufar wannan sabon shiri ita ce gano matasa wadanda Allah yayiwa basira ta kirkire-kirkire a fadin duniya da kuma sauraren yadda zasu raya sashen da ke watsa shirye shirye ga kasashen duniya na BBC ta hanyar da ya ke da tasiri a garesu.

Muna gayyatar duk wani wanda ba ya zaune a Birtania kuma mai shekaru tsakanin 19 zuwa 34 da ya kirkiro wata talla ko jerin tallace-tallace wadanda zasu karfafawa matasa guiwar yin mu'amula tare da BBC. Wanda ya lashe wannan gasa zai samu kyautar £3,000, yayin da kowanne daga cikin mutane biyu masu mara masa baya zai samu kyautar £1000.

Latsa nan domin shiga wannan gasa

Abun la'akari:

Mazauna Birtania basu cancanta shiga wanann gasa ba. Wajibi dukkanin sakonni su kasance da harshen turanci ko kuma idan an yi da harshen gargajiya, a hada da fassara a harshen turanci.

Domin sanin sauran ka'idojin shiga wanann gasa, sai a latsa nan

Ranar fara gasar: 17th October 2013

Ranar fure gasar: 2nd December 2013