Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yawan hadurran mota a Nijeria

Wata kididdigar da Hukumar kiyaye hadurra ta Nijeria, FRSC ta yi, ta nuna cewa, mutane kusan dubu shidda ne suka rasu a bara, sakamakon hadurran da suka faru a kan hanyoyin Nigeriar, kuma wasu dubbai sun jikkata.

Hakan yana nufin mutane goma sha shidda ne ke mutuwa a duk ranar Allah a sanadiyyar hadurra a kan hanyoyin Nijeria, yayinda wasu karin mutanen saba'in da biyu ke samun munanan raunika.

Kusan a kowane mako dai ana samun labarin aukuwar irin wadannan hadurran. A farkon wannan mako ma, kusan mutane ashirin sun riga mu gidan gaskiya a jihar Niger, lokacin da wasu motocin safa biyu suka ci karo da juna, a hanyar Tegina zuwa Lagos.

Wannan matsala ta yawan hadurra a Nijeria dai tana jefa jamaa da abun ya shafa cikin wani mawuyacin hali, ko dai na rashi, ko kuma na doguwar jinya a asibiti, sakamakon hadurran.

To ko wadanne dalilai ne ke janyo wannan matsala? Kuma wadanne matakai ne ya kamata a dauka, don rage aukuwar hadurran?

Kadan kenan daga cikin tambayoyin da jami'an gwamnatin Nijeria da kuma jama'a suka yi kokarin amsawa, a filin namu na Ra'ayi Riga!