An sabunta: 4 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 12:46 GMT

Demokradiyya a cikin jam'iyyun Najeriya

Taswirar Najeriya

Wani batu dake jan hankalin jama'a a fagen siyasar Najeriya a baya bayan nan, shi ne batun demokaradiyya a cikin Jama'iyu.

Koda a ranar Talatar makon nan majalisar dattawa ta kasar ta kira wani zama na jin ba'asin jama'a a kokarin da ta ce tana yi na yi wa tsarin mulkin kasar garanbawul domin inganta harkar zabe a kasar.

Sai dai wasu masu sharhi kan siyasar Najeriyar na cewar batun demokuradiya a cikin Jam'iyyu, ginshiki ne a duk wani gyara da ake son yi ga sha'anin zabe na kasar.

Suka ce yin wannan ne kawai zai iya tabbatar da dorewar Demokaradiyya a kasar saboda a cewarsu wannan shi ne matakin farko a tsanin demokuradiya.

To ko menene muhimmancin tsarin demokuradiyar a cikin jam'iyyu yake da shi da ko kuma ta yaya ne za a iya samar da shi a cikin Jam'iyyun Najeriya?

Mecece matsalar da ke haddasa rashin samun tsarin na Demokuradiya a cikin Jama'iyun?

Wadannan da ma wasu tambayoyin ne zamu nemi amsawa a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako wanda zamu kashe mintuna 60 cif cif tare da ku masu saurare.

Za ku iya aiko mana da lambar wayarku tare da takaitaccen ra'ayinku ta wannan gurbin da ke kasa.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.