Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Demokradiyya a cikin jam'iyyun Najeriya

Wani batu dake jan hankalin jama'a a fagen siyasar Najeriya a baya bayan nan, shi ne batun demokaradiyya a cikin Jama'iyu.

Koda a ranar Talatar makon nan majalisar dattawa ta kasar ta kira wani zama na jin ba'asin jama'a a kokarin da ta ce tana yi na yi wa tsarin mulkin kasar garanbawul domin inganta harkar zabe a kasar.

Sai dai wasu masu sharhi kan siyasar Najeriyar na cewar batun demokuradiya a cikin Jam'iyyu, ginshiki ne a duk wani gyara da ake son yi ga sha'anin zabe na kasar.

Suka ce yin wannan ne kawai zai iya tabbatar da dorewar Demokaradiyya a kasar saboda a cewarsu wannan shi ne matakin farko a tsanin demokuradiya.

To ko menene muhimmancin tsarin demokuradiyar a cikin jam'iyyu yake da shi da ko kuma ta yaya ne za a iya samar da shi a cikin Jam'iyyun Najeriya?

Mecece matsalar da ke haddasa rashin samun tsarin na Demokuradiya a cikin Jama'iyun?

Wadannan da ma wasu tambayoyin ne muka yi kokarin amsawa a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan mako wanda a karon farko muka kashe mintuna 60 cif cif tare da ku masu saurare.

A cikin shirin kuma mun tattauna ne da Dikko Umar Radda, wakilin kungiyar dake neman kawo sauyi a tsarin Shugabanci cikin Jama'iyar PDP, wato PDP Reform Forum.

Akwai kuma Alhaji Farouk Adamu Aliyu tsohon Dan Majalisar wakilai ta Kasa, sannan akwai Hussein Abdu na Kungiyar Action Aid, mai zaman kanta, sannan kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya.

Haka nan kuma mun tattauna tare da Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan tsaro, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso daga Kano da kuma Rabiu Gambo Bakori, Sabon Shugaban Jama'iyar PDP Reshen Jihar Katsina ta wayar tarho.

Akwai kuma wasu daga cikin dinbim masu saurarenmu da muka tuntuba ta wayar tarho suka bayyana albarkacin bakinsu.

Za ku iya ci gaba da muhawara a kan wannan batu a dandalinmu na BBC Hausa Facebook.