An sabunta: 8 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 23:13 GMT

Ra'ayi Riga: Ko wacce rawa kasashen Afrika za su taka a gasar cin kofin duniya?

Kofin kwallon kafa na duniya

Hausawa dai na cewa dadina da gobe saurin zuwa.

Ranar juma'a sha daya ga watan Yuni za a fara gasar cin kwallon kafa ta duniya a Afrika ta Kudu.

Wanda hakan shi ne karo na farko da za a gudanar da wannan gasa a nahiyar Afrika.

Kasashe irinsu Brazil da Najeriya da Argentina da Kamaru da Ingila da Ghana, da sauran kasashe za su baje zaratan 'yan wasa domin kece raini, irinsu Kaka, kakara kwallo da Drogba dodon raga.

Kowacce irin rawa kasashen Afrika zasu taka, ko akwai kasar Afrika da za ta iya yin nasara a wannan gasa.

A shirinmu na ra'ayi riga na wannna makon za mu tattuna ne kan gasar kwallon kafa ta duniyar a Afrika ta kudu.

Domin shiga cikin wannan shirin, Sai ku aiko mana da takaitaccen ra'ayinku da kuma lambar wayar da zamu tuntube ku, ta wannan lamba, +447786202009, ko ta email a hausa@bbc.co.uk, ko ma ta dandalin mu na muhawara da musayar ra'ayi, wato bbchausafacebook. Kada amanta shirin namu awa guda ne cif-cif.

Za kuma ku iya aiko mana da ra'ayinku ta gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.