Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ko wacce rawa kasashen Afrika za su taka a gasar cin kofin duniya?

Hausawa dai na cewa dadina da gobe saurin zuwa.

Ranar juma'a sha daya ga watan Yuni aka fara gasar cin kwallon kafa ta duniya a Afrika ta Kudu.

Wanda hakan shi ne karo na farko da ake gudanar da wannan gasa a nahiyar Afrika.

Kasashe irinsu Brazil da Najeriya da Argentina da Kamaru da Ingila da Ghana, da sauran kasashe za su baje zaratan 'yan wasa domin kece raini, irinsu Kaka, kakara kwallo da Drogba dodon raga.

Kowacce irin rawa kasashen Afrika zasu taka, ko akwai kasar Afrika da za ta iya yin nasara a wannan gasa.

A shirinmu na Ra'ayi Riga na wannna makon mun tattuna ne kan gasar kwallon kafa ta duniyar a Afrika ta kudu.

Kai tsaye mun tattauna da wakilinmu Aliyu Tanko, wanda yake kasar Afrika ta Kudu, domin kawo wa masu sauraro labarin wasanni kai tsaye daga Afrika ta Kudun.

Mun kuma gayyato wasu bakin da suka hada da shahararren tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida; da Ishola Michael daga Bauchi. Muna kuma tattauna da Bashir Jantile, mai sha'awar kwallon kafa kai tsaye a dakinmu na watsa shirye-shirye a London.

Sai Colonel Ibrahim Yacouba, mataimakin shugaban hukumar kula da kwallon kafar kasar FENIFOOT.

Za kuma ku iya sake sauraron shirin a duk lokacin da kuke so a shafinmu na intanet.