Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Achaba: A hana ko kada a hana?

'Yan Achaba, ko Kabu-Kabu, ko Okada ko Going ko kuma ma 'yan arubta kamar yadda wasu ke kiransu - sana'a ce da ke bunkasa sosai a Najeriya, musamman a birane.

Za a iya cewa, shekaru ashirin din da suka wuce, sana'ar acaba ba sananniya ba ce a Najeriya.

Jama'a na sayen baburan ne kawai domin amfanin kansu da iyalansu, ba wai don neman kudi ba.

Amma wasu dalilai da suka hada da bunkasar birane, da matsin tattalin arziki, sun sa jama'a sun maida baburan abun neman kudi.

Sai dai kuma 'yan achaban sun yi kaurin suna, saboda hadurran da ake zargin suna janyowa.

Sai dai wasu gwamnatocin jihohin Najeriyar sun haramta ta, ko takaita ta, saboda a cewarsu, sana'ar na tattare da wasu hadurra.

To an ya kuwa wannan shi ne mafita?

Jama'a da dama sun amsa kiran da muka yi, na neman ra'ayinsu akan sana'ar ta acaba.

Akan haka ne muka tattauna a shirin Ra'ayi Riga na wannan makon.

Mun kuma gayyato Alhaji Mohammed Sani Hassan, babban jami'in kungiyar 'yan achaba ta Najeriya wadda aka fi sani da ACOMORAN. Shi ne kuma shugaban kungiyar 'yan achaban, reshen jahar Kano.

Da kuma Dr Sani Malumfashi, shugaban sashen nazarin zamantakewar dan adam, a jami'ar Bayero dake Kano, wanda yayi bincike mai zurfi dangane da wannan sana'a ta Achaba.

Akwai kuma Alhaji Ahmad Hasan Kogari, kwamandan hukumar kare hadurra ta Nigeria reshen jihar Kano.

Mr Solomon Zan, shugaban kwamitin haramta sana'ar achaba a jahar Plateau.

Da kuma Babangida Shehu Maihula, mazaunin Jos, kuma daya daga cikin shugabannin 'yan Achaba.

Za kuma ku iya ci gaba da muhawara a kan wannan batu, a dandalinmu na BBC Hausa Facebook, wanda za aku iya samu a shafinmu na intanet, wato BBCHausa.com.