An sabunta: 23 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 14:55 GMT

Anya damben da 'yan majalisun Najeriya ke yi na biyan bukatun talakawa ne?

Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya

An dade ana ba hammata iska a majalisar wakilai ta Najeriya

Ba hammata iska dai na neman zama ruwan dare a majalisun dokokin Najeriya.

Irin wannan damben yakai ga rasa rayuka a majalisun Najeriyar, abinda yasa lamarin ke kara jan hankulan jama'a.

Na baya bayan nan shi ne rikicin da ya barke lokacin da wasu daga cikin 'yan majalisar suka yi kokarin gabatar da kudurin neman tsige kakakin majalisar Dimeji Bankole.

Lamarin da yakai ga jiwa wasu daga cikin 'yan majalisar raunuka, ciki kuwa har da mace.

Abin tambaya anan shi ne wai shin 'yan majalisun na yin damben ne domin kare hakkokin wadanda suka zabe su, ko kuma don biyan bukatun su.

Wannan shi ne batun za mu tattauna a filin mu na ra'ayi riga na wannan makon.

Sai ku aiko mana da ra'ayin kodai ta e-mail wato hausa@bbc.co.uk ko ta wannan lambar waya 447786202009 ko ta dandalin mu na wuhawara bbchausa Facebook wanda za ku iya samu a shafinmu na Intanet wato bbchausa.com. Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbin.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.