Me ke janyo yawan mace macen aure a kasar Hausa?

Mutuwar aure

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a kasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na karewa da saki.

Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al'umma ? Me ya kamata a yi don a rage matsalar?

Wasu daga cikin irin tambayoyin da za mu yi kokarin amsawa kenan tare da ku masu saurare a cikin shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.