Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me ke janyo yawan mace macen aure a kasar Hausa?

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a kasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na karewa da saki.

Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al'umma ? Me ya kamata a yi don a rage matsalar?

Wasu daga cikin irin tambayoyin da muka yi kokarin amsawa kenan tare da ku masu saurare a cikin shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Mun kuma gayyato wasu baki na musamman da suka hadara da Bala Muhammad, tsohon abokin aikinmu a sashen Hausa na BBC, kuma daraktan hukumar A Daidaita Sahu ta jihar Kano.

Akwai kuma Dr Isma'ila Zango, Malami a sashen nazarin zamantakewar dan adam a jami'ar Bayero dake Kano.

Sai Hajiya Altine Abdullahi, shugabar kungiyar Zawarawa ta jihar Kano.

Hakazalika akwai Ustaz Hussaini Zakariya, wani malamin addinin Musulunci da kuma Pasto Sani Nomao, shugaban coci-coci na EERN a Niger.

Za kuma ku iya ci gaba da muhawara kan wannan batu a dandalinmu na musanyar ra'ayi da muhawara, wato BBC Hausa Facebook.