Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: A ci gaba da karba-karba a Najeriya ko a daina?

Tun bayan da aka koma mulkin farar hula a Najeriya a shekarar 1999, jam'iyyar PDP wacce ta kafa gwamnati ta dauki matakin rarraba mukamai tsakanin yankunan kasar domin kokarin kawar da korafe korafe da dama gabanin zaben.

Jama'iyar ta kafa Gwamnatoci 3 ta hanyar wannan tsari.

Ana kuma kan wannan tafiya ne har ya zuwa lokacin da Shugaba Umaru Musa Yar'adua ya rasu, abinda wasu ke ganin ya bayar da dama ta a kawar da wannan tsari.

Yanzu haka kuma wannan batu na ta tayar da muhawara musamman a jam'iyyar ta PDP.

To shin me ya kamata a yi da wannan tsari na karba karba na Jama'iyar PDP, ya kamata a ci gaba da shi, ko kuwa a yi fatali da shi?

Wannan shi ne abinda muka tattauna a cikin shirin Ra'ayi Riga na wannan makon!

Mun kuma tattauna a kan wannan batu tare da baki wadanda suka hada da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na Kasa, Chief Solomon Lar, wanda kuma ke son a yi watsi da tsarin na karba karba.

Da kuma Alhaji Lawal Kaita, tsohon gwamnan Kaduna, kuma jigo a jam'iyyar PDP, mai son a ci gaba da tsarin na karba karba.

Sai Dr Abubakar Sadiq, Malami a sashen kimiyyar Siyasa a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria.

Da kuma dimbin masu sauraro da suka shiga cikin shirin, ko dai ta wayar tarho, ko ta e-mail, ko ta sakon text, da ma muhawarar da aka yi tafkawa a dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara, wato BBC Hausa Facebook.

Za kuma ku iya ci gaba da muhawara a dandalin namu na BBC Hausa Facebook a kodayaushe.