Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Nijar ta cika shekaru 50, Ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

Image caption An yi amfani da bikin cikar shekaru hamsin din wajen dasa bishiyoyi domin yakar hamada

A ranar uku ga watan Agustan nan ne Nijar ta cika shekaru hamsin cifcif da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar kasar Faransa.

Daga lokacin zuwa yanzu, an yi gwamnatoci da dama na farar hula da kuma na soja.

Kasar ta kuma fuskanci kalubale da dama da suka hada da juyin mulkin soji har sau hudu, da matsalar tawaye. Sauran matsalolin sun hada da na fari, da na karancin abinci.

An yi juyin mulki hudu a Nijar, 1. a shekarar 1974, da 1996 da 1999, sai kuma shekara ta 2010.

Nijar na da mutane akalla miliyan goma sha hudu, ita ce kuma ta 174 daga cikin kasashe 177 a duniya.

Nijar ta yi fama da matsalar karancin abinci, a shekarun 1970 da 1984 da kuma 2005, lokacin da mutane kimanin miliyan uku suka yi fama da matsalar tamowa. A yanzu ana cewa kusan mutane sama da miliyan bakwai ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a sakamakon fari .

Matsalar rashin aikin yi ga matasa. Matasa su ne sama da rabin al'umar kasar ta Nijar. Matasa da dama da suka kamalam karatunsu babu aikin yi, suna gararamba a tituna, suna aikata laifukka.

To ko daga samun 'yancin kan zuwa yanzu, ci gaban da kasar ta samu ana iya cewa na a-zo-a-gani ne, ko kuwa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba?

Wadannan na daga cikin abubuwan da zamu tattauna tare da ku masu saurare a filinmu na ra'ayi riga na wannan makon.