Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ambaliyar ruwa a wasu kasashen Afrika

Image caption Wannan bala'in ambaliyar ruwa ya ritsa da sassa da dama a Najeriya da Nijar da Chadi

Yanzu haka dai wasu al'umomi a Najeriya da Nijar da Chadi dama sauran wasu kasashe a nahiyar Afrika, sun shiga halin kakanikayi sakamakon ambaliyar ruwa, a 'yan kawanakin da suka wuce.

Za a iya cewa, ambaliyar ruwa ta zama ruwan dare, gama duniya. A kasar Pakistan kawai, sama da mutane miliyan ashirin ne wannan matsala ta shafa.

A jamhuriyar Nijer an yi ambaliyar a wurare da dama da suka hada da Yamai, Maradi, Damagaram da sauransu.

A Najeriya mai makwabtaka da Nijar din ma an sami ambaliyar a jihohin da suka hada da Borno da Jigawa da Sokoto da Kano.

Dubbai sun rasa gidajensu, suna zaune a wurare na wucin-gadi - ko dai na hukuma ko kuma a wajen makwabta da 'yanuwa.

Ruwan kuma ya mamaye gonaki da dama. Mutane dayawa sun rasa rayukansu, miliyoyi kuma sun bar muhallinsu, sannan an yi asarar dukiya mai dimbin yawa.

To ko wanne hali jama'ar da lamarin ya shafa suke ciki, musamman a Najeriya da Niger? Shin wadanne irin matakan rigakafi ne za a iya dauka don tinkarar matsalar ambaliyar ruwan? Shirinmu na Ra'ayi Riga kenan na yau.

Wannan shi ne abin da za mu tattauna a cikin shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

kuma mun gayyato baki kamar su; Barrister Yusuf Mato, Kwamishinan Muhalli na jihar Jigawa da Dr Ado Mukhtar Bichi, Malami a jami'ar kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil, kuma masani kan ilmin labarin kasa - ko Geography da Turanci.

Haka nan kuma mun gayyaci Malam Mustapha Sulaiman wani jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya - NEMA.

A Jamhuriyar Nijar kuma mun samo Laftana Diam Balah, Shugaban Karamar hukumar Tasawa.

Akwai kuma mutanen da matsalar ta shafa kai tsaye. Sannan kuma akwai wasu daga cikinku ku masu saurare ta wayar tarho.