An sabunta: 1 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 10:13 GMT

Ra'ayi Riga: Yiwuwar barkewar anobar kwalara a Najeriya

Kwayar cutar kwalara

Kwayar cutar kwalara

A kwanannan gwamnatin tarrayar Najeriya ta yi gargadi ga gwamnatocin jihohin kasar kan yiwuwar barkewar anobar kwalara a duk fadin kasar, muddin ba'a dauki matakan da su ka dace ba.

Ko yaya girma matsalar ta ke a jihohin ku.? Wani irin matakai ne gwamnatoci ya kamata su dauka domin tunkarar wannan matsala.?

Kadan ke nan a cikin tambayoyin daga cikin irin tambayoyin da za mu amsa tare daku masu saurare a cikin filin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Domin shiga cikin shirin sai ku aiko mana da ra'ayinku a takaice, da kuma lambobin wayoyinku ta wannan lamba: 44 77 86 20 20 09, ko ta email a hausa@bbc.co.uk, ko kuma ta dandalinmu na musayar ra'ayi da muhawara, wato bbchausa facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na Internet, a BBCHAUSA.COM

Zaku iya shiga ta wannan shafin.

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.