Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Magance cutar kwalara a arewacin Najeriya

Image caption Wani mai fama da cutar kwalara

A kwanan baya ne dai Ma'aikatar kiwon lafiya a Najeriya ta yi gargadin cewar baki dayan kasar na fuskantar barazana ta barkewar cutar Kwalara, muddin ba a dauki matakan da suka dace ba.

Ma'aikatar ta ce kawo yanzu cutar ta hallaka mutane fiye da dari uku.

Ma'aikatar kiwon lafiyar ta Najeriya ta ce kawo yanzu kuma dubban mutane ne suka kamu da cutar.

Akasari dai cutar ta fi yin kamari ne a yankunan arewacin Najeriyar. Ko yaya girman matsalar ta ke a jihohin, kuma wadanne matakai ne ake dauka ko ya kamata a dauka na tunkararta?

Wasu kenan daga cikin irin tambayoyin da muka yi kokarin amsawa a cikin Filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Domin gabatar da shirin, mun gayyato baki da suka hada da Alhaji Sulaiman Bello, Minista a ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya, da Kwamishinan kiwon lafiya na Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Yahaya da Dr Muhammad Nasir Muhammad, Jami'i mai kula da Sashen yaki da cututtuka masu saurin yaduwa a ma'aikatar kiwon Lafiya ta Jihar Kano.

Haka nan kuma akwai Alhaji Adamu Abubakar, Jami'in Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Jihar Bauchi.

Mun kuma samu gudummawar wasu daga cikin dinbin masu saurarenmu.